Featured
Dole Ne Wadanda Suke Da Hannu A Kashe Sojojinmu 16 Su Dandana Kudarsu — Tinubu
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya ce duk wadanda suka kashe dakarun sojoji 16 a yankin Okuoma da ke Karamar Hukumar Ughelli a Jihar Delta, za su ɗanɗana kuɗarsu.
A ranar Alhamis ne wasu bata-gari suka yi wa wasu dakarun soji kisan gilla lokacin da suke kokarin sulhunta rikici tsakanin ƙabilar Okuama da Okoloba a Jihar ta Delta.
Bata-garin sun hallaka Kwamandan soji daya, da Manjo biyu, sai Kyaftin daya, da sauran sojoji 12 da kuma wani mutum guda daya.
Tinubu a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ya bayyana kisan a matsayin na “jahilci” da cewa dole a hukunta duk wadanda suke da hannu a lamarin.
