Uncategorized
Wani Dan Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Kansa, Yayin Da Mutum Biyu Suka Raunata
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno a ranar Litinin din nan ta tabbatar da cewa wani dan kunar bakin wake ya raunata mutane biyu a karamar hukumar Biu da ke jihar.
ASP Daso Nahum, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Kasa, NAN, afkuwar lamarin a ranar Litinin.
ASP Daso Nahum ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Lahadi a lokacin da musulmin yanki suke gudanar da sallar dare.
“Mutumin dan kunar bakin wake da ake zargin yana kan hanyar zuwa masallacin ne ya tayar da bam din da ke kusa da zagayen, inda ya kashe kansa.
“An garzaya da wasu mutane biyu da suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani.
“Nan da nan aka tura tawagar jami’an tsaro hadin gwiwa zuwa wurin da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya,” inji shi.
Kakakin ya bukaci jama’a da su kara taka tsan-tsan, musamman a wannan lokaci na Ramadan da akasarin Musulmi ke gudanar da sallar dare.
“Ya kamata jama’a su tabbatar sun yi taka tsan-tsan, kuma kada su yi kasa a gwiwa wajen kai rahoton duk wani abun zargi ga jami’an tsaro,” inji shi. (NAN)
