Uncategorized
Sanusi II Ya Karbi Takardar Fara Aiki A Matsayin Sarkin Kano
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya mika wa Sarki Muhammadu Sanusi II takardar fara aiki a matsayin Sarkin Kano.
Gwamnan ya mika masa takardar aiki ne a wani takaitaccen biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano ranar Juma’a.
A jawabinsa, gwamnan ya ce, ba sabon sarki aka naɗa ba, “kujerarsa da ya tafi na wucin gadi ne yanzu muka dawo masa da ita.”
A ranar Alhamis 23 ga Mayu, 2024, Majalisar Dokokin Kano ta kammala gyaran dokar masarautun jihar, inda ta soke dukkan masarautun biyar da aka kirkiro a zamanin Ganduje.
Kuma a ranar ce Gwamna Abba ya rattaba hannu a bisa dokar ya kuma ba wa sarakunanan masarautun wa’adin sa’a 48 su fice daga fada.
