Uncategorized
Yadda ta kasance a zaman kotu kan rikicin masarautar Kano
Babbar kotun jihar Kano ta dage zaman sauraron kara kan rikicin masarautar Kano zuwa ranar 4 ga watan Yuli da muke ciki.
Babban Antoni janar da majalisar dokokin jihar Kano ne suka shigar da karar ta hanyar lauyansa, Barista Ibtahim Isah-Wangida ina suka nemi kotun da ta dakatar da tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da Sarakunan Bichi da Karaye da Rano da Gaya da aka cire daga ayyana kansu a matsayin Sarakuna.
A yau dai kotun ta sanya domin sauraron dukkan bangarorin, sai dai lauyan dake wakiltar masu kara, Barista Eyitayo Fatogun ya ce sai jiya da yamma lauyan wanda ake kara na farko ya bashi bayanan kariyarsa.
A don haka ya nemi kotun ta basu mintuna 30 domin mika martani ga wanda ake karar.
Sai dai lauyan Aminu Ado Bayero, Abdul Muhammad SAN ya soki hakan inda ya nemi a dage sauraron karar domin basu damar gabatar da martani da bukatunsu.
Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta dage zaman zuwa Jibi Alhamis domin sauraron kowanne bangare da kuma gundarin shari’ar.
