Featured
Ba ‘Yan Najeriya Ne Suka Kashe Sojojin Kasar Ba — Godswill Akpabio
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Talatar nan, ya ce bai yarda cewa ‘yan Najeriya na da hannu a kashe sojoji a jihar Delta ba.
Da yake magana a ranar Talata yayin wata muhawara kan kudiri guda biyu da Sanata Abdulaziz Yar’Adua, na jam’iyyar APC, mai wakiltar Katsina ta tsakiya, da Edeh Dafinone, na APC, mai wakiltar Delta ta tsakiya suka gabatar.
Akpabio ya bayyana cewa wadanda suka kashe sojojin na iya zama ‘yan hayar kisa ne.
Ya ce, “Ba yaki muke yi ba. Bana jin sun fito daga yankin Neja Delta. Suna iya zama ‘yan hayar kisa.”
Tun a watan Janairu ne dai al’ummomin Okuama da Okoloba ke takun-saka kan mallakar wani fili da ke kwance a kan iyakarsu, kuma rikicin da ya barke a tsakaninsu ya kai ga kashe mutane da dama ciki har da yara.
A yayin da wani fada ya sake barkewa a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, rundunar sojin Najeriya ta tura sojoji domin aikin wanzar da zaman lafiya ga al’ummomin. Sai dai an yi wa sojojin kisan gilla, lamarin da ya janyo bacin ran jama’a.
