Connect with us

Labarai

Wata Gobara Ta Tashi A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Na Garkin Block A Jihar Borno

Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Garkin Block da ke Maiduguri a Jihar Borno.

A cewar wani ganau, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Litinin.

Ya ce, cikin kankanin lokaci wutar ta bazu cikin sansanin, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin.

Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) ta ɗauki mataki kan lamarin, inda jami’an kashe gobara suka isa da misalin ƙarfe 5:25 na yamma domin kashe gobarar.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a iya tantance girman barnar da gobarar ta yi ba, haka kuma, ba gano musabbabin tashin gobarar ba daga bangarorin da abin ya shafa.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, sansanin ’yan gudun hijira na Garkin Block na kan hanyar Madinatu da ke cikin birnin Maidugurin jihar Borno.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet