Featured
Jami’ar Tarayya Ta FUOYE Ta Zargi SSANU Da NASU A Mutuwar Wani Dalibi
Wani dalibi mai fama da ciwon asma na Jami’ar Tarayya, da ke Oye Ekiti (FUOYE) ya rasa ransa sakamakon ci gaba da yajin aikin da kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in ta Kasa (SSANU) da takwararta ta (NASU) suke yi.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Tajudeen Opoola, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai.
Tajudeen Opoola ya ce dalibin mai ciwon asma ya mutu ne saboda ya kasa samun kulawa nan take, sakamakon an kulle jami’ar da kwado.
Hukumar makarantar ta zargi SSANU da hannu a rufe baki dayan ayyuka a jami’ar, tare da lura da cewa wasu jami’o’in ba a rufe su kamar FUOYE ba.
Mataimakin shugaban jami’ar ya yi gargadin cewa hukumar ba za ta nade hannunta ba, tare da ba da damar karya doka da oda a fake da yajin aiki.
