Featured
Ƴanbindiga Sun Kashe Wani Dan Siyasa, Tare Da Yin Garkuwa Da Matarsa Da Ƴaƴansa
Wasu ‘yanbindiga sun kai hari ƙauyen Mairuwa da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina a daren ranar Asabar, inda suka kashe Masallata
Akalla mutane biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da wani kuma ya samu rauni.
Aminiya ta rawaito cewa daya daga cikin wadanda suka mutu wani fitaccen mutum ne mai suna Alhaji Lado kuma ana zargin dama shi suke nema.
Wata majiya da ta bayyana marigayin a matsayin ɗan kasuwa, ɗan siyasa kuma babban manomi. Majiyar tace ce an kashe Alhaji Lado ne lokacin da ya ƙi bin umarni daga wadanda suka kashe shi.
Daya daga cikin wadanda suka tsira daga harin ya bayyana cewa maharan sun yi garkuwa da ‘ya’yan Alhaji Lado da kuma matarsa.
