Connect with us

Featured

Katsina: Har yanzu ƴanbindiga na cin karensu ba babbaka

Adaidai lokacin da Muslimi ke azumin watan Ramadana ƴan bindiga a wasu jihohin arewacin Najeriya har yanzu ba su kakkauta ba wajen kai hare-hare kan farar hula.

Na baya-bayan nan shi ne wanda suka kai a ranar Asabar da daddare a garin Mairuwa na karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina kan masu sallah.

Shugaban karamar hukumar Musa Ado Faskari ya tabbatar wa BBC, lamarin inda ya ce an kashe mutum biyu an kuma sace mata biyu.

Shugaban ya shaida wa BBC cewa hare-haren ƴanbindiga na ƙara ƙamari a yankinsu ; ” Wannan al’amari sai dai mu ce Innalillahi Wa Inna ilaihiraji’un saboda kwanan nan mun rasa gane kan al’amarin, abin ya dawo fiye da yadda yake a da, suna ta shiga garuruwa kullum, ko ranar Juma’a sun shiga garin Yanmalamai sun kashe mutum biyu sun tafi da mata.”

Bayanai sun nuna cewa ƴanbindiga sun yi manyan sansanoni a yankin na ƙaramar hukumar Faskari, lamarin da ke haddasa yawan kai hare-hare a garuruwan yankin, “Kuma ko ranar Juma’a da yamma sai da suka kashe wani soja,” cewar Musa Ado.

Shugaban ƙaramar hukumar Faskarin ya shaida wa BBC cewa abin ya ta’azzara kuma suna neman taimako daga gwamnatin tarayya a yankinsu saboda suna cikin matsala babba “wannan al’amari yana neman ya gagari kundila.”

“Mutanen nan dole a shiga cikin daji a yaƙe su ba sai an jira su saboda suna da dabaru kala-kala da suke mana ta’annati.”

Al’ummar yankin ƙaramar hukumar Faskari na cikin fargaba saboda hare-haren ƴanbindiga, lamarin da ya janyo rufe wasu hanyoyin yankin.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet