Featured
Akallah Mutane 13 Sun Rasa Ransu A Wani Hatsarin Motoci Da Ya Auku A Jihar Kogi
Hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta Kasa FRSC a ranar Litinin din nan ta bayyana cewa mutane 13 sun mutu yayin da biyu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Kogi.
Kwamandan hukumar reshen jihar Kogi, Mista Samuel Oyedeji, ya ce hatsarin ya afku ne da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa hatsarin da ya hada da wata motar bas kirar Sharon ta kasuwanci da wata motar siminti, ya afku ne a kasuwar Obajana a kan titin Obajana-Lokoja a karamar hukumar Lokoja.
Kwamandan sashen ya bayyana cewa, motar bas ta Sharon ta tsaya a kusa da kasuwar yayin da wani fasinja yake kokarin siyan wasu kayayyaki, a lokacin da motar siminti ta Shanye birki, ta kuma daki bayan motar.
“Babbar motar ta daki motar bas, nan take ta kama da wuta kusan dukkan fasinjojin da ke cikinta suka kone.
Rahotanni sun ce motar bas din ta nufi Abuja ne daga yankin kudancin kasar.
“Jami’an mu da ke aikin ceto tare da jami’an Red Cross da ‘yan sanda, sun gaza ceto mutanen saboda tsananin gobarar.
“Amma an tattara gawarwakin wadanda abin ya shafa, yayin da aka kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Fisayo, Obajana domin kula da lafiyarsu,” in ji shi.
Oyedeji ya nuna damuwarsa kan yadda babu wani asibiti a Kogi da ya amince a dauki gawarwakin da suka kone domin a ajiye su, wanda hakan na iya tilastawa hukumomi yin jana’iza mai yawa idan har ba a samu wata alaka ba.
Kwamandan sashin, wanda ya bayyana lamarin a matsayin “abin bakin ciki da takaici,” ya gargadi masu ababen hawa da su guji yin gudun wuce sa’a da kuma rashin kula da motocinsu.
A cewarsa, ya kamata masu ababen hawa su rika bincikar ababen hawansu domin tabbatar da komai ya daidaita kafin su fara tafiya don gujewa hadurran mota.
