Connect with us

Featured

Kotu Ta Tisa Keyar Wata Mata Bisa Zargin Kwarawa Mijinta Tafasasshen Ruwa

Wata Kotun Majistire da ke Karamar Hukumar Kontagora a Jihar Neja, ta bayar da umarnin a tsare Amina Abashe da ake zargi da watsa wa mijinta Shehu Abdullahi tafasasshen ruwa.

‘Yan sanda sun gurfanar da wadda ake zargin ne a gaban kuliya bisa laifin yi wa mijinta mummunan rauni da ya saba wa sashe na 245 na kundin dokoki shari’a.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Danladi Marafa, ya shaida wa kotun cewa matar da ake zargi ta kwararawa mijinta ruwan zafi sakamakon wani sabani da ya gifta a tsakaninsu.

Sai dai bayan karanto ƙunshin tuhumar da ake yi wa matar da ake ƙara, ta musanta aikata laifin.

Lauya mai gabatar da kara, ya bukaci da a tisa keyar matar da ake tuhuma zuwa gidan gyaran hali, domin bai wa masu ƙara damar duba lafiyar wanda abin ya shafa da a yanzu yake samun kulawa a Babban Asibitin Kontagora.

Ya kuma bukaci a ɗan ba su lokacin domin tabbatar da hujja da kare matar da ake tuhuma.

Alƙaliyar Kotun, Khadijah Dauda, ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Afrilun da muke ciki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet