Connect with us

Featured

Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Rabon Fom Din JAMB Kyauta Ga Daliban Sakandire

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon fom din shiga makarantun gaba da Sakandire JAMB kyauta ga daliban makarantun sakandire 6,500 a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati a Kano.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai.

Sanarwar ta rawaito Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da rabon tallafin yana mai cewa, “a yayin da muke raba fom din JAMB kyauta a yau ga ‘yan jihar Kano 6,500, bari na tabbatar da cewa wannan karimcin shine. alama ce ta jajircewar gwamnatinmu wajen saka hannun jari a makomar yaranmu.

“Mun yi imanin cewa ilimi ginshikin ci gaba ne kuma ta hanyar karfafa wa dalibanmu, yaranmu za su samu ilimi mai inganci, muna aza harsashin samar da ci gaba mai dorewa ga jiharmu ta Kano,” in ji Gwamna Abba.

Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen karin haske kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen bunkasa fannin ilimi a cikin watanni goma da suka hada da; sake dawo da tallafin karatu na kasashen waje, biyan kudin rajista ga ’yan asalin Kano da ke karatu a Jami’ar Bayero, Kano, sake bude cibiyoyi 21 na koyan sana’o’i.

Sauran a cewar Gwamnan sun hada da; rage kashi 50% na kudaden rajista a manyan makarantun jihar, Bada Kudi don Tallafawa Ilimin Yara mata da Yara, daidaita kudaden rajista na NECO, NABTEB da NBAIS.

Jaridar Kano Focus ta rawaito cewa  Abba ya bukaci daukacin wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da damar da suka samu tare da yin kokari wajen ganin sun samu nasara a harkar karatunsu inda ya ce su yi aiki tukuru domin mayar da mafarki gaskiya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet