Featured
Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Zargin Ciyo Bashin Naira Biliyan 14.26
Gwamnatin Zamfara ta musanta zargin ciyo bashin Naira biliyan N14.26, tana mai cewa bashi ne na 20 billion da aka ciyo a gwamnatocin da suka gabata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnatin Dauda Lawan bata ciyo wani bashi acikin gida ko wajen kasar ba.
“Akwai bukatar mu yi wa Alumma karin haske game da rahoton da hukumar kula da bashi ta Najeriya ta fitar cewa gwamnatin Zamfara taci bashi na N14.26 billion
“Gwamnatin Zamfara bata taba yunqurin ciyo bashi ko tunkarar majalisar jiha ko ta tarayya akan a sahale mata ta ciyo bashi ba.
“Yana da kyau a gane cewa An ciyo bashi a gwamnatocin d suka shude na N20 billion. Amma aka gaza karbar kudin gaba daya.
“Gwamnatin qarshe da ta shude ta karbi N4 billion acikin 20 billion din da aka ranto domin aikin tashar jiragen daukar kaya ta Zamfara, duk da batayi amafani d kudin akan aikin ba.
“Ragowar 16 billion cikin 20 billion da aka ciyo bashi shine 14.26 billion wanda yaja hankalin hukumar kula da bashi ta Najeriya, kuma kudin ya ragu ne saboda matsalar hauhawar farashi.
“Kuma shi wannan kudi yanzu haka yana Asusun gwamnati, kuma za ayi amfani dashi wajen aikin tashar.
