Featured
Gwamnatin Kebbi Za Ta Bai Wa Maniyyatan Jihar Tallafin Naira Miliyan 1
Gwamnatin Jihar Kebbi ta sahale a bawa kowanne maniyyaci daga cikin maniyyatan jihar 3,344 tallafin naira miliyan daya.
Kwamishinan yada labarai da Al’adu na jihar, Hon. Yakubu Ahmed Birnin Kebbi shi ya bayyanawa manema labarai hakan a jiya bayan wani zaman gaggawa da sukayi a taron majalisar zartarwa.
Ya bayyana cewa” Za a bawa kowanne maniyyacin jihar naira miliyan daya ba tare da bata lokaci ba”.
Ragowar maniyyatan jihar da suka riga suka cika kudin aikin hajjin nasu, su ma za a basu Naira miliyan dayar.
