Featured
Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Tantance Sabbin Kwamishinonin Da Abba Ya Aika Mata
Majalisar dokokin jihar Kano ta tantance tare da tabbatar da sunayen kwamishinoni hudu da Gwamna Abba Kabir-Yusuf ya aika mata a ranar Talatar nan.
Majalisar dai, bayan kammala gabatar da zamanta na farko a ranar Talatar a Kano, ta rusa kwamitin tantance wadanda gwamnan jihar ya aika mata tun da farko.
Wadanda aka tabbatar sun hada da: Mustapha Rabi’u-Kwankwaso, da Adamu Aliyu-Kibiya, da Abduljabar Garko da kuma Shehu Aliyu-Yanmedi.
Daga baya shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini (NNPP-Dala), ya gabatar da kudirin tabbatar da sunayen wadanda aka zaba, wanda shugaban marasa rinjaye, Labaran Madari na (APC-Warawa) ya goyi bayansa.
Shugaban majalisar, Ismail Falgore (NNPP-Rogo), bayan da aka kada kuri’ar amincewa da kudurin, ya tabbatar da wadanda aka tantance sannan ya umurci magatakarda da ya mika hukuncin ‘yan majalisar zuwa ofishin gwamna.
A ranar 26 ga watan Maris ne Gwamna Kabir-Yusuf ya gabatar da jerin sunayen sabbin mutane hudu da aka nada a ma’aikatu hudu.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, ma’aikatun sune; Ma’aikatar Harkokin jin kai, Ma’aikatar Wutar Lantarki da Sabunta Makamashi, Ma’aikatar Tsaro ta Cikin Gida da Ma’aikatar Ma’adinai.
