Featured
Wani Direban Golf Ya Rasa Ransa A Wani Hatsarin Mota A Kano
Wani Direban mota kirar Golf ya rasa ransa a wani mummunan hatsarin da ya afku a Gadar Damagari, unguwar Zoza a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano.
Wani ganau Ashiru Murtala ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na dare, inda ya ce Wani mai babur ne daga Karaye zuwa Garin Rogo a ya yi karo da Golf din, kuma nan take direban motar ya rasu.
Babban kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano Labaran Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya danganta hatsarin da gudun wuce gona da iri.
Abdullahi ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa da mutane biyar wadanda suka hada da maza hudu da mace daya.
Ya shawarci jama’a masu tuka ababen hawa da su guji tukin mota ba tare da duba lafiyar ta ba, da yi gudun wuce sa’a da kuma keta dokokin zirga-zirgar ababen hawa.
