Featured
Watanni 4 Kenan Da Harin Tudun Biri, Gwamnati Bata Cika Alkawarin Diyya Ba
Yau Laraba 3 ga watan Aprilu ake cika watanni 4 cuf da faruwar kuskuren harin da Sojoji suka kai garin Tudun Biri na karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, sai dai har zuwa yanzu gwamnati ba ta biya diyyar ko da mutum guda cikin dimbin mutanen da harin ya kashe ba.
A ranar 3 ga watan Disambar bara ne, wani hari da Sojojin Najeriya suka kai da jirage marasa matuki ya kashe tarin mutanen da ke tsaka da taron mauludi a garin na Tudun Biri lamarin da ya tayar da hankalin al’ummar kasar nan.
Tun kwanaki kalilan bayan faruwar lamarin gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta sha alwashin biyan diyyar daukacin mutanen da harin sojojin ya kashe da yawansu ya haura 120 baya ga sake gina kauyen baki daya.
Wani bincike ya gano yadda gwamnatin jihar Kaduna ta faro ginin masallachi wanda aka yi a dai dai wajen da harin ya kashe masu mauludin, sai kuma titin da ake shiga garin da shima aka faro aikinsa baya ga rijiyar burtsatse, sai dai babu batun biyan diyya da kuma sake gina garin daga bangare gwamnatin Tarayya.
Haka zalika har zuwa yanzu al’ummar garin basu iya samun kudaden da wasu daidaikun mutane suka tallafa musu da shi ba, ko da ya ke an umarce su da su bude asusun ajiya na banki don sanya musu kudaden.
RFI ya gano cewa kawo yanzu an sallami ilahirin mutanen da suka jikkata a harin Sojojin na ranar 3 watan Disamba, duk da cewa har yanzu suna ziyartar asibiti don duba wasu raunuka da suka samu lokaci zuwa lokaci.
