Featured
Matasa A Najeriya Sun Fi Ra’ayin Zama Mataimaka Na Musamman Ga Shugaban Kasa Ko Gwamna – Sowore
Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar AAC a zaben 2023 Omoyele Sowore yace matasa a najeriya sun fi sha’awar zama mataimaka na musamman ga Shugaban kasa ko gwamnoni.
Sowore ya bayyana haka ne a wata hira da yayi a shirin siyaya na gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Dan gwagwarmayar ya bayyana wannan dabi’ar ta matasan yan Najeriya ga yan siyasa ne bayan an rantsar da dan shekara 44 a matsayin sabon shugaban kasa a Senegal.
Faye dai an rantsar da shi ne a taron da shugabannin Afrika dayawa suka halarta a Dakar ranar Talata.
Da yake magana akan wannan cigaba, Sowore yace matasa a wannan kasar tamu su burin su shine su zama mataimaka na musamman ga gwamnoni da sauran shugabanni.
“Matasan mu sun zama yan a bi yarima a sha kida, sun fi bukatar zama mataimaka na musamman ga sanatoci da gwamnoni.
“Banga wani buri da suke dashi na zama jagorori ba.
Sowore yace akwai bukatar matasa a Najeriya su zama jarumai a siyasa domin kawo irin wannan sauyi na Senegal a Najeriya.
“Samartaka tana da matuqar amfani ga kwakwalwa dole ana bukatar shugaba jajiryacce wanda ya cancanta kuma xai iya daukan nauyin da yake kan sa ba wanda zai karar da rabin lokacin sa a Asibiti ba” a cewar sa.
