Connect with us

Featured

Kungiyar Kwadago NLC Ta Yi Allah Wadai Da Karin Kuɗin Wutar Lantarki A Najeriya

Kungiyar kwadago ta Kasa NLC da waɗansu kungiyoyin fararen hula sun yi tir da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da tsarin wuta mai daraja ta ɗaya wato Band A.

’ya’yan kungiyar NLC, sun ce duk dalilan da jami’an gwamnati suka bayar kan karin kudin ba hujjoji ba ne.

A cewarsu, ko a ƙasashen da aka ci gaba, ana tallafa wa wasu ɓangarori kamar man fetur da wutar lantarki.

A jiya Laraba ne dai Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta sanar da ƙarin kuɗin kilowatt na wuta daga Naira 68 zuwa Naira 225.

Wannan karin ga masu amfani da tsarin Band A da ke samu wuta na tsawon sa’o’i 20 a kullum za su riƙa biyan Naira 135,000 kowane wata.

A taron da mataimakin shugaban NERC, Musiliu Oseni ya yi da manema labarai a Abuja, ya ce karin zai shafi kaso 15 na masu amfani da wutar lantarki miliyan 12 a Najeriya.

Kungiyar Kwadago Ta Najeriya Za Ta Ɗauki Matsaya

Shugaban yada labarai a shedikwatar NLC, Benson Upah, ya ce Ƙungiyar ta su za ta ɗauki matsaya kan mummunar ta’asar da aka yi na ƙarin kuɗin wuta.

Benson ya ce, za su sanar da matsayarsu idan masu ruwa da tsaki a kungiyar sun zauna.

“Shawarar da gwamnati ta yanke ba mafita bace a harkokin kasuwancin ƙasar nan.

“Abin da in aka yi wasa zai kore masu saka hannun jari daga ƙasashen ƙetare a Najeriya.

Ya kara da cewa, “Mutanen da za su ci riba daga wannan tashin hankali da jama’a za su shiga su ne Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF.

“Abin tausayi! Za mu dawo gare ku a kan wannan batun nan gaba kaɗan, bayan masu ruwa da tsaki a kan wannan mataki na ƙungiyarmu sun zauna.”

Wani tsohon shugaban NERC, Sam Amadi, ya ce ƙarin kuɗin wutar lantarki zai haifar da satar wutar kuma zai karfafa rashawa da almundahana a sashen.

Da yake magana a gidan Talabijin na Trust, Amadi ya ce, “Idan ka ƙara kudin wutar lantarki zuwa matakin da mutane ba za su iya ba, hakan zai ƙara janyo satar wuta ta bayan fage, cin hanci da rashawa, kuma a ƙarshe, ma’aikatu za su yi asara fiye da kima.

Sannan kuma, “eh gaskiya ne akwai kwakkwaran dalili na ƙara kuɗin harajin saboda matsalar kuɗin da ake samu da kuma karin farashin iskar gas da za a sayar wa kamfanonin samar da wutar lantarki.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftdinamobetgrandpashabet girişgrandpashabetdinamobetGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantcasinolevantcasinolevantcasinolevantholiganbetjojobetgrandpashabetgrandpashabetsahabetsahabetonwinonwinmarsbahismatadorbetonwinsahabetsuperbetinmarsbahisjojobetgrandpashabetgrandpashabetholiganbettipobetsekabetsekabetholiganbetsahabetsahabetcasibomcasinolevantbetgarantibetciovdcasinosekabetmatbetimajbetcratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahissekabetgrandpashabetjojobetpusulabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabetGrandpashabet