Connect with us

Featured

Kotu Ta Dakatar Da Muhuyi Magaji Daga Mukaminsa

Kotun da’ar ma’aikata ta dakatar da Shugaban Hukumar karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhyi Magaji, sakamakon zarge-zargen da ake yi masa na rashin da’a da kuma cin zarafin jami’an gwamnati.

Muhuyi Magaji wanda ke fuskantar tuhume-tuhume daga zargin cin hanci da rashawa zuwa bayyana kadarorinsa na karya da karbar cin hancu, an gurfanar da shi a Abuja ranar Alhamis.

Kotun ta amince da bukatar dakatar da shi, inda ta umarce shi da ya fice daga matsayinsa har zuwa lokacin da za a yanke hukunci.

Tun da farko dai gwamnatin jihar Kano ta maka gwamnatin tarayya a gaban babbar kotun jihar bisa abin da ta bayyana a matsayin cin zarafi da cin mutuncin shugaban PCACC da wasu hukumomin tarayya uku ke yi.

Wannan ci gaba ne ga gayyata da aka aika zuwa PCACC da hukumar gudanarwar hukumar daga 2011 zuwa yau.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, mai magana da yawun CCB, Veronica Kato, ta tabbatar da dakatar da Magaji da CCT ta yi.

Sanarwar ta ce, “Kotun da’ar ma’aikata ta dakatar da Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji, a yau Alhamis a Abuja bisa tuhume-tuhume 10 na almundahana da hukumar da’ar ma’aikata ta shigar a kansa a 16 ga Nuwamba, 2023.

“Da yake zartar da hukuncin, shugaban kotun da’ar ma’aikata, Justice Danladi Umar, ya tabbatar da cewa kotun tana da hurumin sauraron karar.

“Ya bayyana cewa Muhuyi Magaji ba zai iya ci gaba da gudanar da ayyuka da ofishin sa ba yayin da yake fuskantar shari’a don gujewa tsoma baki a lamarin.

“Wannan tasa zai yi jiran kammala shari’ar. Daga nan aka dage sauraron karar har zuwa ranar 7 da 8 ga watan Mayun 2024, domin sauraren karar.”

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet