Featured
Gwamna Abba Ya Kori Sunusi Surajo Kwankwaso Daga Muƙaminsa
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sallami Mai Ba Shi Shawara Kan Harkokin Siyasa, Sunusi Surajo Kwankwaso, daga muƙaminsa.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya naɗa Mustapha Bakwana a matsayin sabon Mai Ba Shi Shawara Kan Harkokin Siyasa domin maye gurbin Sunusi Surajo Kwankwaso.
Daraktan yaɗa labarai na gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-tofa ne ya sanar da hakan, ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, sai dai ba a fitar da cikakkun bayanai dangane da dalilin sauyin ba, inda aka ce za a bayyana ƙarin bayani nan gaba.
