Featured
Ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a Saudiyya
Hukumar kula da ganin Wwata ta ƙasar Saudiyya, ta sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Shawwal ba a ƙasar.
Hakan na nufin za a azumci ranar Talata, inda Ramadanan bana za a cike ya zama an yi azumi 30 kenan.
Don haka ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2024 ce za ta yi daidai da 1 ga watan Shawwal na shekarar 1445 bayan hijira.
A kan haka ne hukumar gudanarwar ƙasar Saudiyya, ta umarci jama’ar ƙasar da su cike azuminsu zuwa 30, sannan su yi idi a ranar Laraba.
