Connect with us

Featured

Ana Zargin Wasu Mahara Sun Kutsa Kai Cikiin Sakatariyar Gwamnatin Oyo

Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kutsa kai cikin sakatariyar Gwamnatin Jihar Oyo, inda suka yi yunkurin ƙwace iko da ofishin gwamna da kuma majalisar dokokin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewar ana zargin maharan da ƙoƙarin ƙwace iko tare da kafa tutar Ƙasar Oduduwa a gidan gwamnatin jihar.

Wani ganau, ya ce maharan na sanye da kayan aikin soja, sannan sun rufe fuskokinsu da wani ƙyalle.

Majiyar ta ce jami’an ’yan sanda da haɗin gwiwar dakarun Amotekun ne suka yi ɗauki-ba-daɗi da maharan.

Rahotanni sun ce maharan sun isa sakatariyar ne cikin motoci ƙirar bas, ɗauke da wata tuta da ke nuni da suna rajin kafa wata ƙasa ne.

Mutanen da ke kusa da sakatariyar sun jiyo ƙarar harbe-harben bindiga na tsawon lokaci.

An tura ƙarin jami’an tsaro da yawa ciki har da sojoji, inda suka mamaye sakatariyar, suka tare duk wasu ƙofofin shiga da fita na sakatariyar.

An sauya wa ababen hawa da ke zirga-zirga daura da sakatariyar zuwa wata hanya.

Jami’an tsaro sun kama wasu a yayin harin, amma har yanzu ba su tabbatar da adadin mutanen da suka kama ba.

Majiyoyin sun ce an yi nasarar kama wasu daga maharan ne, biyo bayan taho-mu-gama da suka yi da jami’an tsaro.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet