Connect with us

Featured

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Matashi Bisa Zargin Dabawa Abokinsa Wuka A Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana cewa ta shirya kama wani matashi dan shekara 18 da ya daba wa abokinsa wuka har lahira a wata takaddama.

An bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na rundunar a ranar Lahadi.

A cewar rundunar, an garzaya da mutanen biyu zuwa asibiti bayan sun yi artabu da wuka, inda aka tabbatar da mutuwar Mutum daya.

Sanarwar ta ce, “Halayyar rashin haƙuri abu ne mai haifar da nadama.

“Usman Umar mai shekaru 18 a yanzu haka yana kwance a daya daga cikin asibitocin mu, yana karbar magani, yana dauke da munanan raunuka a kansa.

“Duk da haka jami’an tsaro na ‘yan sanda suna dako domin cafke shi bisa laifin kisan kai ta hanyar daba wa abokinsa Usman Abubakar wuka, mai shekaru 18 da haihuwa, wanda yanzu haka yana dakin ajiye gawa saboda wata ‘yar takaddama.

“Ku daina yaƙi a tsakaninku, kuma ku yi haƙuri.”

Kakakin rundunar, SP Suleiman Nguroje, ya kara da cewa rundunar tana gudanar da bincike kan lamarin kuma za a yi karin bayani a nan gaba.

Ya rubuta, “Su biyun sun yi rigima da juna ta hanyar amfani da wukake suna kai wa kansu hari. ‘Yan sanda sun isa inda aka garzaya da su zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwar daya.

“Hukumar tana bincike, za mu yi cikakkun bayanai nan ba da jimawa ba.” In ji sanarwar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet