Featured
Rikicin Da Ya Dabaibaye APC Kan Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Ganduje Ya Dauki Sabon Salo
Rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC mai mulkin Kasa a Kano ya dauki sabon salo a daidai lokacin da sabbin shugabannin Mazabar Ganduje suka sake dakatar da shugaban riko na jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Bayan haka, sabon shugabancin da ya fito daga gundumar Ganduje, a karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar ta yi ikirarin cewa ita ce halastacciyar shiyar, wadda aka zabe ta bisa doka da inganci a ranar 31 ga watan Yulin 2021.
Da yake jawabi ga manema labarai a Kano, a ranar Lahadin da ta gabata, sakataren Mazabar Ganduje, Ja’afar Adamu Ganduje, wanda ya yi magana a madadin wasu shugabannin zartaswa 11 ya bayyana dakatarwar da aka yi wa tsohon gwamnan Kano bisa zargin cin zarafin jam’iyya da Ganduje ya nuna wanda ya kai ga rarrabuwar kawuna da gazawar jam’iyyar a zaben da ya gabata.
Adamu wanda yayan Ganduje ne kuma ya zargi Dr. Abdullahi Umar Ganduje da tayar da rikici wanda ya kai ga gaggarumin bangaranci guda biyu a Mazabar, inda ya jawo wa jam’iyyar abun kunya a zukatan jama’a.
Hakazalika sakataren ya yi zargin cewa shugaban jam’iyyar APC na kasa ba ya biyan kudaden jam’iyyar da ya kayyade.
A cewar Adamu, “Mu ne sahihan shugabannin Mazabar Ganduje kuma mun yi watsi da karar tare da sanya wa Dakta Abdullahi Umar Ganduje sabuwar dakatarwa saboda wasu dalilai.
“Da farko mun dakatar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga cikin mambobin jam’iyyar saboda haifar da rikicin cikin gida a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a matakin Mazaba. Wani babban dalilin da ya sa nagartattun shuwagabannin zartarwa suka yanke shawarar dakatar da Ganduje shi ne batun ayyukan cin hanci da rashawa a lokacin zabukan 2023, wanda ya haifar da gazawar jam’iyyar a jihar”.
Adamu ya jaddada cewa wadannan bangarori biyu da ke ikirarin cewa su exco ne daga Mazabar Ganduje karya ne da yaudara
Adamu ya sake nanata cewa shugabannin Mazabar Ganduje na gaskiya ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an hukunta bangarorin biyu tun da farko sun yi magana da manema labarai cewa su ’yan Mazabar ne.
