Connect with us

Featured

Wasu Matane Uku Sun Rasa Ransu Yayin Dauko Wayar Salula A Masai

Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane uku a garin ’Yar Gwanda da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta jihar a lokacin da suka yi kokarin shiga masai don dauko wata wayar hannu da ta fada.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano Saminu Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa tunda farko wayar salular wani magidanci mai suna Danjuma Black dan kimanin shekara 60 ta fada cikin masai, inda ya shiga da niyyar dauko ta.

Da aka ji shiru shiru bai fito ba sai dansa mai suna Ibrahim ya shiga da niyyar ceto mahaifinsa, shi ma bai fito ba.

“Hakan ya sa wani mai suna Aminu Key Guy shi ma ya shiga da niyyar ceto su, shi ma dai shiru bai fito ba.

“A nan ne mutum na hudu mai suna Abbas Alhassan ya shiga da niyyar ceto wadancan mutane ukun shi ma dai kamar sauran bai fito ba.

“Daga nan ne aka kira jami’anmu da ke Tsanyawa inda suka zo suka fito da dukkanin mutane hudun.”

Saminu ya kara da cewa “An yi nasarar fito da mutum na karshen da ransa, amma ukun farkon sun fita daga hayyacinsu.”

Saminu Abdullahi ya ce bayan sun fito da mutanen ne suka mika su ga ofishin ’yan sanda na Tsanyawa inda aka kai su asibiti, inda a nan ne likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet