Addini
Gwamnatin Borno Ta Sakewa Hukumar Alhazan Jihar Matsayi
Gwamnatin jihar Borno ta bayyana shirin mayar da hukumar jin dadin alhazai ta jihar zuwa babbar hukumar.
Gwamna Babagana Zulum, wanda ya sanar da hakan a ranar Asabar a Maiduguri, babban birnin jihar, ya ce matakin zai tabbatar da yin gaskiya da rikon amana a cikin kudaden gwamnati.
Ya yi magana ne a lokacin da yake kaddamar da kwamitin alhazan jihar mai mutane 21, wanda Sanata Kaka Lawan ya jagoranta.
“Dole ne mu sake tsara hukumar jin dadin Alhazai. Za mu mayar da hukumar zuwa babbar hukuma,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya lura cewa kafa hukumar zai rage kashe kudaden da gwamnati ke kashewa tare da tabbatar da yin gaskiya da rikon amana.
Zulum ya bada tabbacin cewa kwamitin zai inganta jin dadin alhazai a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024.
Gwamnan ya bukaci ‘yan kwamitin da su yi aiki tukuru domin cimma bukatar alhazai.
Ya kuma bayyana dalilin da ya sa aka sauya mataimakin gwamna Umar Kadafur wanda ya kasance shugaban hukumar alhazan jihar tsawon shekaru hudu.
“Tun da na hau kujerar gwamnan Borno a shekarar 2019, mataimakin gwamna ne shugaban kwamitin aikin Hajjin mu.
