Featured
‘Yan Sandan Abuja Sun Kama Wasu Mutum Biyu Bisa Laifin Satar Mota
Jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun kama wasu fitattun barayin mota guda biyu, Ibrahim Haliru mai shekaru 45 da Babangida Mohammed mai shekaru 27.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Josephine Adeh, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X ranar Lahadin nan.
Bafarawa Ya Koka Da Yadda Sai Sun Nemi Izinin ‘Yan Bindiga Sannan Suke Noma
A cewar sanarwar, wadanda ake zargin, daya tsohon mai laifi ne daga jihar Kano, dayan kuma dan asalin garin Mararaba na jihar Nasarawa ne. an kama su ne bisa laifin satar motoci da dama a babban birnin tarayya Abuja da kewaye.
Sanarwar ta ce, “Jami’an rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, a ranar 23 ga watan Afrilu, 2024, da misalin karfe 3:00 na rana, sun kama wasu manyan ‘yan fashin nan guda biyu, Ibrahim Haliru dan shekara 45 (wanda aka yankewa hukunci) a jihar Kanoda Babangida Mohammed mai shekaru 27 a garin Mararaba na jihar Nasarawa, dangane da wasu satar motoci da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka yi a babban birnin tarayya Abuja da kewaye.
“Wadanda ake zargin, wadanda ke cikin jerin sunayen ‘yan sandan da ake nema ruwa a jallo a ‘yan watannin da suka gabata, an kama su ne tare da taimakon leken asiri na otel a jihar Nasarawa a lokacin da suke karbar kudaden da suka aikata.
