Connect with us

Featured

Bafarawa Ya Koka Da Yadda Sai Sun Nemi Izinin ‘Yan Bindiga Kafin Suyi Noma

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya koka da cewa sai al’ummar mahaifarsa sun nemi izinin ’yan bindiga sannan suke iya noma gonakinsu.

Da yake magana a kan tsadar kayan abinci a Kasar nan, Bafarawa ya danganta matsalar da rashin tsaro, yana mai cewa ’yan bindiga ne ke zabar gonakin da ake nomawa a mahaifarsa da ke karamar hukumar Isa.

Tsohon dan takarar shugaban kasar a karkashin jam’iyyar PDP, ya shaida wa ’yan jarida a ranar Litinin cewa shi kansa dole ya hakura da noma a gonarsa mai fadin hekta 10,000 saboda rashin tsaro.

Wani Magidanci Ya Hallaka Matarsa Ta Aure Har Lahira Da Wuka

“Ina da gona mai fadin sama da hekta 10,000 a Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, da nake noman masara tun a shekarar 1979, amma yanzu ban isa inje ba saboda ’yan bindiga,” in ji shi.

Acewar Bafarawa, “matsalar tsaro ce ta kawo tsadar kayan masarufi saboda manoma ba sa iya zuwa su noma gonakinsu.

“A baya na taba jan hankalin gwamnati game da yiwuwar tashin farashin kayan abinci saboda wannan matsalar amma suka ki sauraron shawarar.”

‘Yan Sandan Abuja Sun Kama Wasu Mutum Biyu Bisa Laifin Satar Mota

A karshe ya ba da shawarar hadin kai tsakakin gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi wajen magance matsalar tsaro, musamman a yankin Arewa.

A cewarsa, “Gwamnatocin jihohi kadai ba za su iya ba sai da taimakon gwamnatin tarayya.”

Hakazalika, ya yi kira ga shugabanni da su farka daga barcinsu domin magance matsalar kafin ta gagari kundila.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet