Featured
NLC Ta Bukaci Lalle Gwamnati Ta Biya Mafi Karancin Albashi Na Naira 615,000
Kungiyar kwadago ta Kasa NLC ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara mafi karancin albashi zuwa Naira 615,000 ko kuma ta fuskanci Turnaki.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin ta yi karin shekaru biyar a kan wa’adin yin ritayar ma’aikata.
Shugaban kungiyar kwadago ta Kasa (NLC), Joe Ajeaoro ya ce mafi karancin albashi N615,000 ne zai yi daidai da halin da ake ciki na matsin tattalin arzikin da tsadar rayuwa a kasar.
Joe Ajaero da takwaransa na Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikata (TUC), Festus Osifo ne suka gabatar da wannan buƙata a dandalin Eagle Square da ke Abuja, yayin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya.
Sun bukaci gwamnati ta gaggauta kammala shirin aiwatar da sabon mafi karancin albashin kafin karshen watan Mayu.
Shugabannin kwadagon sun ce rashin aiwatar hakan zai haifar da fito-na-fito tsakanin gwamnatin da ma’aikata a ƙasar nan.
A daren ranar Talata NLC ta bayyana karin 25% da 35% na albashin ma’aikata da gwamnati ta ayyana a matsayin “ɓata lokaci.”
A cikin jawabinsa na ranar Laraba, Kwamared Ajaero ya ce: “A wannan lokaci, ’yan uwa, ina so in sanar da ku cewa, yanzu muka fara yakin neman gyaran mafi karancin albashin ma’aikata a ƙasar nan.
“Mun tabbatar da dukkan bangarori sun samu wakilci, kuma tattaunawa ta yi nisa. Mun gabatar da bukatarmu ta N615,000 a gaban abokan tattaunawarmu, yanzu su muke sauraro.
“Amma idan ba a kammala tattaunawa a kan mafi karancin albashi ba zuwa karshen watan Mayu, lallai za a ga abin da ba a so daga gare mu,” in ji Ajaero.
