Connect with us

Featured

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Sace Dagatai Guda Biyu A Jihar Kaduna

 

Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa an sace dagattai biyu da ke kan hanyarsu daga Kakangi zuwa Birnin-Gwari.

’Yan bindigar sun kuma kai hari a Maraban Agyaro inda suka sace wasu mutane a Kakangi da Kisaya, kuma suka kashe wasu mutane takwas a karamar hukumar ta Birnin Gwari.

Maharan sun kai hari yankin ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Alhamis, inda suka yi awon gaba da wasu manoma hudu da ke aiki a gonakinsu.

Wata majiya a yankin ta ce an sace mata shida a kauyen.

Dan majalisar da ke wakiltar gundumar Kakangi a majalisar dokokin jihar, Yahaya Musa Dan Salio, ya ce dukkan mutane takwas da aka kashe ’yan Kakangi ne.

“Eh, yanzu ne aka yi min waya cewa an sace mutum biyu a mazabata tare da kashe wasu takwas. Duk wadanda aka kashe ’yan Kakangi ne,” in ji shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya ce zai yi bayani idan ya kammala bin diddigin abin da ya faru a yankin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet