Connect with us

Featured

Wasu ‘Yan Zamfara Sun Bukaci EFCC Ta Sake Duba Zargin Bello Matawalle

 

Wasu mutane da suka bayyana kan su a matsayin ‘yayan jam’iyyar APC daga Jihar Zamfara sun yi tattaki zuwa ofishin hukumar EFCC dake Abuja, inda suke bukatar ganin an sake kakkabe kurar dake takardun zargin da ake yiwa tsohon gwamnan jihar kuma ministan tsaro Bello Matawalle na karkata kudaden da suka kai naira biliyan 70 lokacin a mulkinsa.

Masu zanga zangar da suka hada da mata da maza dauke da allunan da ke dauke da rubuce-rubuce daban daban sun mika takardar korafin su ne ga jami’in hukumar, Wilson Uwujaren wanda ya wakilci shugaban hukumar.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa a watan Mayun bara, EFCC tace tana gudanar da bincike kan tsohon gwamnan a kan karkata akalar kudaden jihar da yawansu ya kai naira biliyan 70 na kwangiloli, amma daga bisani sai maganar ta kwanta, yayin da aka kuma nada Matawalle a matsayin minista.

EFCC tace wadannan makudan kudade da jihar ta karbo bashi domin gudanar da wasu manyan ayyuka a sassan kananan hukumomin jihar sun yi batan dabo ta hanyar wasu ‘yan kwangila na bogi da suka karbe su ba tare da gudanar da wani aiki ba.

Hukumar bata yi nasarar kama tsohon gwamnan ko kuma gurfanar da shi a gaban kotu bayan saukarsa daga jagorancin jihar ba, a lokacin da ya fadi zabe.

Matawalle wanda yanzu haka karamin ministan tsaro ne ya yi ta cacar baka da shugaban EFCC na wancan lokaci Abdurasheed Bawa kafin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga mukamin sa.

Ya zuwa yanzu dai bangaren ministan da ke APC bai mayar da martani ba dangane da wannan zanga zanga zuwa ofishin EFCC.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet