Featured
Zargin Batanci: Abduljabbar Da Lauyansa Basu Bayyana A Gaban Kotu Ba
Babbar Kotun Jihar Kano ta sake zama domin sauraren shari’ar daukaka karar da Abduljabbar Kabara da ke kalubalantar hukuncin Babbar Kotun Musulunci da ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Sai dai a zaman kotun na yau Alhamis ba a ga mai kara ba wato Malam Abduljabbar Kabara ko kuma lauyansa.
Lauyan gwamnati, Barista Bashir Saleh, ya mika rokonsu a gaban kotun a kan ta fadada musu lokaci don yin suka ga rokon da masu kara suka yi.
Kotun karkashin jagorancin Masu Shari’a Nasiru Saminu da Aisha Mahmood, ta amince da rokon lauyoyin gwamnati inda ta dage shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Mayu, 2024.
Idan za a iya tunawa dai Abduljabbar Kabara ya mika wa kotun rokonsa guda biyu inda yake kalubalantar kundin shari’ar da aka yi masa a kotun kasa, cewa ba cikakke ba ne.
Haka kuma Abduljabbar ya yi zargin cewa a cikin kundin shari’ar akwai kwange na wata sadara.
