Featured
Kakakin Majalisar Dokoki Zai Aurar Da Mata Marayu Guda 100
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji, ya bayyana shirin aurar da wasu marayu mata 100 da suka rasa iyayensu sakamakon harin ‘yan bindiga a karamar hukumar Mariga.
Sarkindaji ya bayyana hakan ga manema labarai a Minna, babban birnin jihar a ranar Juma’a.
Shugaban majalisar ya yi alkawarin biyan sadaki tare da sayo duk wasu kayan da ake bukata don daurin auren.
Hakan tasa aka zabo ‘yan matan da za a aurar da su cikin tsanaki daga cikin ‘yan mata 170 da aka mika sunayensu.
An Kaddamar Da Bincike Kan Zargin Wasu Jami’an Tsaro 2 Da Cin Zarafin Dalibar Jami’a
Shugaban wanda ke wakiltar mazabar Mariga, ya bayyana shirin a matsayin wani shiri na karfafawa mazabarsa da nufin rage radadin talauci.
Ya kuma bayyana cewa Gwamnan Jihar Neja Mohammed Umar Bago da Sarkin Kontagora Alhaji Mohammed Barau za su kasance masu kula da marayun matan a yayin daurin auren gama gari.
Ana sa ran babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, zai halarci taron wanda aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Mayu a Bangi, hedkwatar karamar hukumar Mariga.
