Connect with us

Featured

Kungiyar masu hada magunguna ta yi zanga-zangar adawa da cin zarafin da NDLEA ke yi a Kaduna

Kungiyar masu harhada magunguna ta Najeriya reshen jihar Kaduna ta yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da yadda jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA suke cin zarafi tare da karbar kudi.

Masana harhada magunguna sun yi zargin cewa hukumar na tsoratarwa, da yin kame ba bisa ka’ida ba tare da neman cin hanci daga mambobinta.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, Shugaban Hukumar PSN na Jihar, Sunday Okoh, ya bayyana cewa cin zarafi da hukumar NDLEA ke yi wa masu harhada magunguna a jihar ya zama abin da ba za a iya jurewa ba.

Kakakin Majalisar Dokoki Zai Aurar Da Mata Marayu Guda 100

Okoh yace “Muna so mu yi amfani da wannan dama wajen janyo hankalin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da masu ruwa da tsaki da sauran jama’a kan yadda hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ke cin zarafin mambobin kungiyar (PSN).

Kungiyar ta bukaci hukumar ta NDLEA da ta mutunta hakkin majinyata tare da baiwa masu harhada magunguna damar gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta basu dama.

Ya kara da cewa, “Kame masu harhada magunguna da hana neman beli da sunan binciken da ake yi, da kwace magungunan da aka rubuta a kantin magani da kuma sanya hatimi a kan kantin magani ba zai hana mu ci gaba da gudanar da ayyukan mu ba”.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet