Featured
EFCC Ta Haramta Amfani Da Dala A Ofisoshin Jakadancin Ketare Dake Najeriya
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Kasa ta’annati EFCC ta haramta duk wata hadar-hadar kudin kasashen ketare a ofishin jakadanci kasashen waje dake Najeriya a hukumance.
Hukumar a kokarinta na farfado da darajar Kudin Kasar nan Naira ta ce daga yanzu wajibi ne ofisoshin jakadancin kasashen waje da ke Najeriya su rika karbar Naira yayin da mutum zai biya wasu kudade.
Ta cikin wata takardar shawara data aikewa ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar, ta ce lokaci yayi da ya kamata a fara amfani da Naira a Ofishoshin jakadancin ketare dake Najeriya.
Takardar mai dauke da kwanan watan 5 ga watan Afrilun da ya gabata ta ci gaba da cewa wannan ta’ada na daya daga cikin abinda ya sanya ‘yan Najeriya ke nuna Kauna da kuma mutunta dala fiye da Naira, abinda ke taka muhimmiyar rawa wajen durkushewar darajar ta.
Hukumar ta kuma kafa hujja da wata sadarar doka data kafa babban bankin Najeriya wadda itama ta yi bayani kan tilasta amfani da Naira a harkokin yau da gobe matukar ana cikin Najeriya.
A don haka ne hukumar ta shawarci ‘yan Najeriya da su bijirewa duk wani ofishin jakadancin ketare da ya bukaci su biya dala ko kudin ketare yayin da suke hada-hadar kudi.
