Featured
Taron Jin Ra’ayin ‘Yan Kasa Ya Karawa Sojoji Wa’adin Mulki A Mali
Taron jin ra’ayoyin ‘yan kasa na Mali da aka gudanar ya amince da karawa gwamnatin soji wa’adin shekaru kafin shirya zabe da mika gwamnati ga hannun farar hula.
Wadanda suka halarci zaman mafi yawan su sojoji ne kuma sun amince da baiwa Kanal Assimi Goita damar ci gaba da jan ragamar kasar, tare da bashi damar tsayawa takara a duk lokacin da aka shirya gudanar da zabe.
Sai dai kuma ana ganin wannan zama tamkar dai na jeka na yi ka ne la’akari da yadda fararen hula da dama suka kaurace masa, tare kuma chachakar tsari da kuma yarjejeniyoyin da aka cimma a karshen sa.
Mali dai ta fada hannun ‘yan juyin mulki ne a shekarun 2020 da kuma 2021, kuma sun yi alkawarin shirya zabe ba tare da wani bata lokaci ba, sai dai hakan bata samu ba sakamakon yadda suke jan kafa da kuma karawa kansu wa’adin ci gaba da zama kan karagar mulki.
