Connect with us

Featured

Gwamnatin Kaduna Ta Sanar Da Kashe Wani Jagoran ‘Yan Fashin Daji (Dogo Bangaje)

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce jami’an tsaro sun kashe wani jagoran ‘yan fashin daji mai suna Dogo Bangaje tare da abokan aikinsa uku.

Wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Jihar ta bakin Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Punch ne suka yi nasarar kashe ‘yan bindigar a ƙaramar hukumar Giwa.

“Dakarun sun fara kai samame ƙauyen Tumburku da kuma Sabon Sara, inda suka kashe mutum biyu tare da ƙwace abubuwa da suka haɗa da babura, da wayar hannu, da sigari, da layoyi, da jakunkunan leda cike da man fetur,” in ji kwamashinan.

“An kai irin wannan hari a ƙauyen Basurfe, inda dakarun suka murƙushe ‘yan fashin dajin da suka yi musu ƙofar rago kuma suka kashe biyu daga cikinsu. Daga baya kuma suka gano wani sansaninsu a cikin daji.

“Daga cikin abubuwan da aka ƙwato akwai bindigar AK-47, da harba-ruga, da jakar harsasai 16, da rediyo biyu, da bam, da pbabur, da wayar hannu, da ƙwayoyi, da sigari, da sauran kayan kiwon lafiya.”

Aƙalla mutum 1,097 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilun da ya gabata – akasarinsu sakamakon hare-haren ‘yanbindiga – a cewar wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting ya fitar a yau Litinin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet