Featured
Kano: Taron Gangi Ya Rikide Zuwa Rikicin Daba, Inda Mutane Uku Suka Rasa Ransu
Wasu mutane uku sun rasa rayukansu a wani rikicin da ya barke tsakanin wasu ’yan daba a unguwar Darmanawa da ke Karamar Hukumar Tarauni a jihar Kano.
Rikicin ya faru ne bayan wani magidanci ya shirya taron gangi domin murnar auren ’ya’yansa.
Daga nan ne ’yan daba suka yi amfani da wannan dama don gwada kwanji.
Daga bisani abin ya rikide zuwa kazamin fadan da ya yi ajalin mutane uku.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, SP Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce an sanar da su cewa ana rigima a Darmanawa, sun aika jami’ansu inda daga bisani suka samu labarin cewa mutane uku sun rasa rayukansu.
SP Haruna ya bayar da tabbacin kama mutumin da ya shirya gangin da kuma wasu mutane biyu da ke anguwar.
