Connect with us

Featured

Gwamnatin Kogi Ta Sanar Da Kubutar Da Wasu Daliban Jami’a Shida Da Aka Sace

Gwamnatin jihar Kogi ta sanar da ceto wasu dalibai shida da aka yi garkuwa da su na jami’ar (CUSTECH) da ke Osara a jihar Kogi.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ya ce sabbin daliban da aka ceto sun kawo adadin daliban da aka ceto zuwa 20.

“Bayanan sun nuna cewa akwai dalibai hudu har yanzu ba a gano su ba,” in ji shi.

Wasu ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji 5 Da Wasu Fararen Hula Da Dama A Katsina

Wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen sun tsere da munanan raunuka a yayin wani artabu da jami’an tsaro.

“An ceto dalibai tara da farko yayin da aka gano wasu biyar da safe. Iyalan daliban shida da aka ceto sun tabbatar da cewa daliban sun isa gida,” inji shi.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka shiga jami’ar da daddare inda suka yi garkuwa da wasu dalibai da ke karatun jarabawar da za su yi. Daga bisani gwamnatin jihar ta ce jami’an tsaro sun fara aikin ceto nan take.

Kano: Hukumar Hisbah Ta Kama Maza Da Mata 20 Suna Wanka Tare

Yayin da sace-sacen ya ke kara yawa a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin kasar tun farko, ‘yan bindigar sun karkata zuwa wasu sassan Najeriya, inda suke kai hare-hare a kauyuka da kuma sace matafiya domin neman kudin fansa.

Duk da irin tabbacin da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro suka bayar na kawo Ƙarshen matsalar, ‘yan ta’addan na ci gaba da yin barna a sassan kasar nan.

Lamarin dai ya sa ‘yan Najeriya da dama da gwamnonin jihohin kasar suka bukaci a samar da ‘yan sandan jahohi domin dakile matsalar rashin tsaro.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet