Featured
Kano: Hisbah Ta Kama Maza Da Mata 20 Suna Wanka Tare
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 20 da suka hada da maza da mata bisa laifin yin wanka tare.
Jami’an Hukumar bangaren ‘Operation Kau Da Badala’ sun kama su ne a wani wurin shakatawa da ke kan titin ring road sakamakon korafin da mazauna yankin suka yi.
Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya ce laifin ya saba wa dokar Hisbah domin ta hana hada jinsin biyu a cikin ruwa domin yin wanka.
Ya nuna damuwarsa kan lamarin, wanda a cewarsa, za a iya maye gurbinsa da wani aiki mai fa’ida da za a samu lada a wajen Ubangiji.
Ya ce idan an kammala bincike za a hukunta wadanda ake zargin, sannan ya yi kira ga iyaye da masu kula da su da su sanya ido sosai kan harkokin ‘ya’yansu.
