Featured
Malaman Addinin Musulunci Sun Caccaki Ministar Mata Kan Kokarin Hana Auren Marayu A Neja
Zauren malaman addinin musulunci na Najeriya yace yana goyon bayan aurar da yan mata marayu 100 da aka shirya yi a jihar Neja da ke tsakiyar kasar, yana mai bayyana cewa auren bazai hana matan karatu ba.
Zauren ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar juma’ah, inda ya bayyana aurar da yan matan a matsayin matakin da zai taimaka musu wajen tsare mutuncin su.
Wannan sanarwa dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ministar mata ta Najeriya Barista Uju Kennedy Ohanenye take cewa ma’aikatar ta ta shirya baiwa yan matan 100 sabuwar rayuwa da mayar da su makaranta da kuma koya musu sana’o’i.
Tun da farko ministar tayi zargin cewa matan da za a aurar basu kai shekarun aure ba, inda ta shigar da kara kotu tana neman a hana kakakin majalisar dokokin jihar Neja aiwatar da shirin aurar da yan mata marayu a jihar.
Sai dai sanarwar malaman wadda shugaban zauren malaman Aminu Inuwa da sakatare Injiniya Bashir Adam Aliyu suka sanya wa hannu tace kamata yayi ministar ta fahimci yanayin al’adu a kasar kafin daukar irin wannan mataki.
A cewar sanarwar kamata yayi ministar tayi amfani da ofishinta wajen magance laifukan da ake yawan aikatawa akan mata maimakon hana shirin aurar da su.
A karshe majalisar tace abinda shugaban majalisar dokokin jihar Neja yayi na daukar nauyi aurar da marayun wannan abin a yaba masa ne, domin yayi dukkan abinda ya kamata.
