Featured
Kotun Koli Ta Bai Wa Jihohi 36 Kwana 7 Su Kare Kansu
Kotun kolin Najeriya ta umarci gwamnonin jihohin kasar nan 36, da su kare kansu cikin kwanaki bakwai kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar na neman cikkaken cin gashin kai ga kananan hukumomi 774 na kasar nan.
Kotun ta kuma umarci Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a Lateef Fagbemi (SAN), bayan ya samu kariya daga gwamnonin, ya gabatar da amsarsa cikin kwanaki biyu.
Mai shari’a Garba Lawal, ya bayar da wannan umarni ne a ranar Alhamis yayin da yake yanke hukunci kan bukatar rage wa’adin da Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ya yi.
Kotun kolin ta ce dole ne a kammala gabatar da dukkan matakai da musayar bayanai da suka kamata a kan lokaci, inda ta sanya ranar 13 ga watan Yuni dan sauraron karar.
