Connect with us

Featured

NAHCON Ta Gargadi Alhazai Kan Shigar Da Haramtattun Kaya Saudiyya

Hukumar aikin hajji ta kasa  NAHCON ta sake gargadar maniyyata aikin hajjin 2024 da su guji safarar haramtattun kwayoyi, goro da sigari ko sauran abubuwan da aka haramta zuwa kasar Saudiyya.

Hukumar tace Saudiyya kasa ce da ke amfani da dokokin addini da al’adu, kuma tana da tsauraran dokoki kan fataucin miyagun kwayoyi tare da hukuncin kisa ga duk wanda ta samu da laifin karya dokar.

NAHCON tayi wannan gargadi ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakiyar daraktan hulda da jama’a, Fatima Sanda Usara a ranar Alhamis a Abuja.

NAHCON ta tunatar da maniyyatan cewa manufar tafiyar su zuwa Saudiyya Ibada ce, dan haka kada su shagaltu da aiyukan da zasu keta alfarmar Hajjin su, inda tace hajji lokaci ne na addu’o’i da ya kamata a tunkare shi cikin girmamawa da mutunta dokoki da al’adun kasar mai masaukin baki.

Ta shawarci maniyyatan da su rika lura da jakunkunan su a tashoshin jiragen sama, don gujewa saka musu kayan da aka haramta a cikin kayan su ba tare da sanin su ba. Sannan ta bukaci Alhazai da su kare martabar su da ta kasar su, inda ta gargadi cewa duk mutumin da aka kama yana safarar kayayyakin da aka haramta ba wai kawai ya jawo wa kansa abin kunya ba, har ma da zubar da mutuncin al’ummar sa.

Hukumar ta kuma yi kira ga hukumomin Alhazai na jihohi da su hada kai da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da sauran hukumomin da ke da alaka da su, wajen ganin an kama mutanen da ke shirin safarar kayayyakin da aka haramta a Saudiyya don gujewa abin kunya da kuma jinkirin da ba’a bukata yayin tantance su.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet