Addini
NAHCON ta zaɓi kamfanonin jirage 5 da za su yi jigilar maniyyata a 2027
Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta ce ta zaɓi tare da amincewa da kamfanonin jiragen sama biyar da za su yi jigilar maniyyatan Najeriya a aikin Hajjin 2027.
Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ta gudanar da jerin tantancewa kan kamfanonin jiragen, ciki har da tsarin tsaron fasinjoji da ingancin jiragen.
Read Also : ADC ta zargi hukumomin tsaro da yunƙurin kama Rauf Aregbesola
NAHCON ta ce ta yi amfani da ƙa’idojinta, da na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya da kuma Hukumar Sufurin Jiragen Saudiyya wajen tantance kamfanonin.
Kamfanonin da suka yi nasara a tantancewar su ne Air Peace Limited, Flynas, Max Air Limited, Saudi Air da UMZA Limited, waɗanda za su yi jigilar maniyyatan Najeriya a Hajjin 2027.
