Featured
ADC ta zargi hukumomin tsaro da yunƙurin kama Rauf Aregbesola
Jam’iyyar ADC mai hamayya a Najeriya ta zargi hukumomin tsaron ƙasar da kitsa shirin kama sakatarenta na ƙasa, Rauf Aregbesola, gabanin zaɓen gwamnan Jihar Osun da ke tafe.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta ce ta samu “sahihan bayanan sirri” kan shirin kama Aregbesola, wanda kuma ya taɓa zama gwamnan Jihar Osun.
Read Also : Gwamnatin Sokoto za ta kashe Naira Biliyan 1.7 domin Sayen Babura ga jami’an tsaro
Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta ko wata hukumar tsaro a ƙasar da ta tabbatar da wannan zargi. Jam’iyyar ta ce zargin shirin kama shi na matuƙar tayar da hankali.
ADC ta danganta hakan da abin da ta kira ci gaba da tsoratarwa da muzgunawa, da kuma amfani da cibiyoyin gwamnati ta hanyoyin da ba su dace ba wajen muzguna wa ƴan hamayya. Aregbesola ya kasance gwamnan Osun daga 2010 zuwa 2018, kafin ya zama ministan cikin gida a gwamnatin Buhari.
