Featured
Gwamnatin Sokoto za ta kashe Naira Biliyan 1.7 domin Sayen Babura ga jami’an tsaro
Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kashe Naira biliyan 1,759,250,000 domin sayen babura ƙirar Bajaj guda 1,000 da za a raba wa hukumomin tsaro domin ƙarfafa yaƙi da ƴanbindiga.
Daraktan Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ya ce Majalisar Zartarwar jihar ce ta amince da buƙatar, domin ƙara wa jami’an tsaro kayan aikin da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.
Read Also : ASUU ta umarci malaman jami’o’i su shirya tsunduma yajin aiki
Bawa ya ce sayen baburan zai ƙara tallafa wa motocin yaƙi masu sulke guda 62 da gwamnatin jihar ta saya kwanan nan kan Naira biliyan 27, waɗanda aka raba wa hukumomin tsaro domin ƙarfafa ayyukan sintiri da tabbatar da tsaro.
Baya ga tsaro, Majalisar Zartarwar jihar ta amince da wasu ayyuka a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, ruwa da bunƙasa sana’o’i, ciki har da gyaran makarantu da cibiyoyin lafiya, da kuma samar da kayan koyon sana’a ga cibiyoyin mata 46 da ke ƙananan hukumomi 23 na jihar.
