Featured
Tinubu Ya Fadi A Filin Eagles Square Lokacin Da Yake Kokarin Hawa Mota
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Ya Fadi a kasa a Lokacin da yake kokarin hawa motar da za ta zagaya dashi domin karbar fareti a Filin Eagles Square.
Shugaba Tinubu, Wanda ya gabatar da Jawabi ga Yan Najeriya a Safiyar Larabar nan, ya wuce filin na Eagle Square domin karbar fareti.
Sai dai a lokacin da yake hawa motar da aka tanadar masa domin zagayawa, Sai Shugaban ya zame ya fadi, duk da yayi kokarin kare kansa don kar ya fadi amma hakan bai yiwu ba, Sai dai mataimakan sa sunyi gaggawa inda suka takmaka masa ya koma ya tsaya.
A karshe an cigaba da Zagayawa da Tinubu a Motar, inda yayi ta dagawa dandazon Alummar da suke filin Hannu.
