Featured
Sallah: Rundunar Tsaron Fararen Hula ta Civil Defense Za Ta Baza Jami’ai 3,168 Don Tabbatar Da Tsaro
Rundunar tsaron fararen hula ta Civil Defence ta sanar da shirin baza jami’anta sama da dubu 3 domin tabbatar da tsaro a yayin bukukuwan babbar Sallah a jihar Kano.
A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SC Ibrahim Abdullahi ya fitar a ranar Juma’a ya ambato Kwamandan rundunar, Mohammed Lawal Falala na cewa za su hada kai da hukumomin tsaro wajen tsare kadarorin al’umma.
A don haka ne rundunar ta sanar da tura jami’ai 3,168 a bukukuwan na sallah.
“Rundunar ta amince da tura jami’ai 3,168 domin bada tsaro a yayin bikin Babbar Sallah a jihar Kano. Jami’an za su yi aiki ne tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na ‘yan sanda da DSS da FRSC da KAROTA wajen tabbatar da doka da Oda”, inji sanarwar.
Rundunar ta Civil Defence ta bukaci al’ummar jihar Kano da su bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen gudanar da bukukuwan na Babbar Sallah cikin lumana.
