Featured
NDLEA ta kama muggan kwayoyi da aka yi shirin raba su yayin bukukuwan Sallah a Kano
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama kwayoyi guda 230,600 a wani sumame da ta kai na kwanaki 3 a hanyar titin Zaria zuwa Kano da kuma wuraren da ake ta’ammali da muggan kwayoyi.
Wuraren da hukumar ta kai samamen sun hada da filin wasa na Sani Abacha da Kaskasara da Dorayi da Makabartar Dan Agundi da Brigade da kuma filin Idi.
A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar rashen jihar Kano, Sadiq Muhammad Maigatari ya fitar, ya ce yayin samamen sun kama mutane 106 da kuma manyan dilolin kwaya 11.
Sanarwar ta kara da cewa an kama tabar wiwi da Solisho da Madarar Suck and die da kwayoyi masu bugurwa wadanda aka so yin amfani dasu a yayin bikin Sallah.
Kwamandan hukumar ta NDLEA na jihar Kano, Abubakar Idris Ahmed yayi alkawarin ci gaba da yaki da ta’ammali da muggan kwayoyi a fadin jihar.
Sannan daga karshe ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin Sallah.
